Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Neja Zata Samar Da Hanyar Ci Gaba Mai Dorewa

0 101

Gwamnatin jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) da bankin Alternative domin cigaban jihar.

 

MOU da aka rattaba hannu a Abuja, ta shafi muhimman sassa kamar ilimi, lafiya, noma, sufuri, makamashi, da samar da ababen more rayuwa.

 

Gwamna Mohammed Bago ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar, inda ya nuna farin cikinsa da shirye shiryen cibiyar hada-hadar kudi da jihar domin bunkasa noma. Gwamna Bago ya yi nuni da cewa, jihar na shirin bayar da hayar kayan aiki masu motsi da kasa kamar su Caterpillar, bulldozers, pale loaders, da graders don shirya kadada miliyan 4.5 na noma a cikin shekaru 10 masu zuwa.

 

Bago ya ce, “a halin yanzu jihar tana tattaunawa da Almarai, wani kamfanin sarrafa kiwo na kasar Saudiyya, domin samar da masana’antar Alfalfa. An fahimci darajar tattalin arzikin shukar, kuma ana ci gaba da kokarin yin nazari kan abubuwan da ke tattare da sinadarin gina jiki don samun ingantacciyar shuka iri.”

 

Gwamnan ya umarci mataimakin shugaban ma’aikatan sa da kuma shugaban kamfanin Neja Foods Limited da su hada hannu da hukumar kudi domin samun nasarar da ake bukata.

 

Babban Daraktan Bankin Alternative, Garba Mohammed, ya bayyana damammakin dalar Amurka miliyan da dama na zuba jarin noma a jihar. Wani abokin tarayya na kasa da kasa yana son zuba jarin dala miliyan 65 don noman rake, samar da ayyukan yi da samar da wutar lantarki da sauran kayayyaki.

 

Wani abokin hadin gwiwa daga Hadaddiyar Daular Larabawa a shirye yake ya saka hannun jari tsakanin dala miliyan 1 zuwa dala miliyan 10 don fitar da shukar Alfalfa, wanda ke bukatar kadada 100,000 don noma. Dangane da batun siyan kayan aikin motsa kasa, Mohammed ya ba da shawarar cewa gwamnatin jihar ta samu Ijarah Sukuk daga kasuwar babban birnin kasar na tsawon shekaru 5 zuwa 7, inda ya jaddada rage farashi da kuma mayar da hannun jari ba tare da wani babban farashi daga jihar ba.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.