Take a fresh look at your lifestyle.

Jami’ar Maiduguri Ta Samu Cibiyar Kirkira Da Harkokin Kasuwanci

0 70

Daya daga cikin manyan jami’o’in Najeriya, Jami’ar Maiduguri yanzu tana alfahari da sabuwar cibiyar kirkire-kirkire da kasuwanci ta duniya.

 

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya kaddamar da cibiyar ta kudi naira biliyan biyu a ranar Asabar a wani bangare na ziyarar da ya kai jihar Borno.

 

Wani hamshakin dan kasuwan Najeriya, Alhaji Abdul-Samad Rabiu, babban jami’in gudanarwa na rukunin kamfanonin Bua ne ya gina ginin.

VP Shettima ya bayyana fatan Cibiyar za ta bunkasa harkokin ilimi da kasuwanci na daliban jami’ar.

 

Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Aliyu Shugaba, wanda ya godewa kungiyar Bua bisa wannan karamcin da ta yi, ya tabbatar da cewa ginin zai yi amfani sosai.

 

Cibiyar tana da damar baiwa mahalarta damar ƙaddamar da haɓaka sabbin kamfanoni waɗanda za su inganta rayuwarsu da ta al’umma.

 

Bude cibiyar kirkire-kirkire da kasuwanci ya biyo bayan taron karo na 24 na jami’ar da ake yi yanzu haka a cibiyar taron kasa da kasa na jami’ar Maiduguri.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.