Take a fresh look at your lifestyle.

Malesiya Ta Bada izinin Bizar Shiga Kasar-Kyauta Ga Sinawa Da Al’umar Indiya

0 104

Malesiya za ta ba da izinin shiga kasar ba tare da biza ba ga ‘yan Sin da Indiya na tsawon kwanaki 30 daga ranar 1 ga Disamba, a cewar Firayim Minista Anwar Ibrahim.

 

Anwar ya bayyana hakan ne da yammacin ranar Lahadi a lokacin da yake jawabi a taron jam’iyyarsa ta People’s Justice Party, kuma bai bayyana tsawon lokacin da za a yi amfani da takardar izinin shiga kasar ba.

 

Sin da Indiya sune kasuwanni na hudu da na biyar mafi girma a Malesiya bi da bi.

 

Bisa kididdigar da gwamnati ta fitar, Malesiya ta sami yawan masu yawon bude ido miliyan 9.16 tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara, tare da 498,540 daga Sin da 283,885 daga Indiya. Wannan idan aka kwatanta da masu shigowa miliyan 1.5 daga Sin da 354,486 daga Indiya a daidai wannan lokacin na 2019, kafin barkewar cutar.

 

Matakin dai ya biyo bayan irin wannan matakan da makwabciyarta Thailand ta dauka na bunkasa muhimman harkokin yawon bude ido da kuma kara habaka tattalin arzikinta, inda ‘yan Sin da Indiya ke cikin wadanda aka kebe a bana.

 

A halin yanzu, ‘yan Sin da Indiya dole ne su nemi takardar izinin shiga Malaysia.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *