Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan sandan Saliyo Sun Fitar Da Hotuna Da Sunayen Wadanda Ake Nema 34

0 43

 ‘Yan sandan kasar Saliyo sun wallafa hotuna da kuma sunayen mutane 34 maza da mata da ake nema ruwa a jallo a rikicin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 20 a Freetown babban birnin kasar ranar Lahadi.

 

Maza 32 da mata biyu da aka lissafa a matsayin “wadanda suka gudu” sun hada da sojoji masu aiki da masu ritaya, jami’an ‘yan sanda da farar hula.

 

Sanarwar ‘yan sandan da aka wallafa a shafukan sada zumunta ta yi alkawarin bayar da “kyakkyawan tukuici” ga duk wanda ya ba da bayanan da ya kai ga kama su.

 

A ranar Lahadin da ta gabata, Freetown ya gamu da arangama ta sa’o’i da dama tsakanin jami’an tsaro da wasu da ba a san ko su waye ba, wadanda suka yi kokarin kutsawa cikin rumbun ajiyar makamai na sojoji.

 

An kai wa gidan yarin na tsakiya da sauran wuraren gyaran jiki hari kuma da alama fursunoni da dama sun tsere.

 

Rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan ashirin, a cewar majiyoyin soji da na bincike.

 

Sojojin da ke aiki ko kuma masu ritaya ne suka shirya su, in ji kakakin rundunar.

 

Hukumomin ba su fayyace dalilai ko makasudin su ba.

 

Abubuwan da suka faru sun kara dagula kallon wani juyin mulki a yammacin Afirka, wanda tun shekarar 2020 aka yi juyin mulki a Mali, Burkina Faso, Nijar da Guinea, dukkansu mambobin ECOWAS.

 

 

 

Africanews/Ladan Nasidi.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *