Sanatocin Arewacin Najeriya Sun Bukaci Gwamnatin Mulkin Sojan Nijar Da Ta Dawo Da Mulkin Dimokuradiyya
Kungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya ta yi kira ga gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar da ta fitar da jadawalin mika mulki tare da maido da mulkin dimokradiyya a kasar.
A cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron kungiyar da aka gudanar a zauren majalisar dokokin kasar a Abuja, shugaban kungiyar Sanata Abdul Ahmed Ningi, ya bayyana damuwar shi kan yadda ake ci gaba da hada-hadar sojoji a fagagen dimokuradiyya a wasu kasashen Afirka.
Sanata Ningi ya ce kamata ya yi gwamnatin mulkin soja a Jamhuriyar Nijar ta tsara jadawalin mika mulki da bai kamata ya wuce shekaru biyu ba don baiwa kasar da ke yammacin Afirka damar komawa tafarkin dimokradiyya.
“Kungiyar Sanatocin Arewa sun yi Allah-wadai da kakkausar murya kan tsoma bakin sojoji a fagagen dimokuradiyya a [sassan] na yankin yammacin Afirka. Taron ya yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Nijar, wanda ke makwabtaka da Najeriya. Mun roki gwamnatin mulkin soja a Nijar da su yi biyayya ga bukatun wasu kasashe ta hanyar sako shugaba Mohammed Bazoum da iyalanshi domin su zabi kasar da yake so inda zai nemi mafaka. Kungiyar Sanatocin Arewa ta kuma bukaci gwamnatin mulkin soja a Nijar da ta samar da jadawalin mika mulki wanda ba zai wuce shekaru biyu ba,” inji Sanata Ningi.
Kungiyar ta kuma bukaci shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, da ya janye takunkumin da aka kakaba wa kasar.
Kungiyar ta ce, wannan takunkumin yana janyo wa ‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba a jamhuriyar Nijar wahala.
“Mun roki shugaban kasa kuma babban kwamandan sojojin tarayyar Najeriya da kuma shugaban kungiyar ECOWAS, Bola Ahmed Tinubu, da cewa, a wani lamari na taimakon jin kai, mu maido da wutar lantarki a Jamhuriyar Nijar. Muna kira ga Nijar da Najeriya [mu tuna] cewa mun kasance ‘yan’uwa. Mun kasance abokan tarayya, kuma mun kasance ‘yan Afirka,” in ji shi.
Idan dai ba a manta ba a watan Agustan shekarar 2023 ne gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakarta da jamhuriyar Nijar biyo bayan mamayar da sojoji suka yi a kasar.
Shugaba Tinubu ne ya bayar da umarnin rufe iyakokin kasa kamar yadda shawarar da kungiyar ECOWAS ta cimma.
Kimanin jihohi bakwai na arewacin Najeriya, wato Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno suna iyaka da Jamhuriyar Nijar.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply