Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Anambra Na Farko Ya Rasu

99

Gwamnan jihar Anambra na farko Cif Chukwuemeka Ezeife ya rasu yana da shekaru 85 a duniya.

 

 

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Cif Rob Nwakaire Ezeife, a madadin iyalan Ezeife, inda ya bayyana cewa dattijon dan kabilar Igboukwu ya rasu a cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Abuja a yammacin ranar Alhamis.

 

 

 

“A madadin daular Ezeife ta Igbo-Ukwu, ina so in sanar da daukaka darajar dan mu mafi girma, Okwadike, Dr. Chukwuemeka Ezeife, CON. Gwamnan Jihar Anambra na farko.

 

 

 

An haifi Ezeife ne a Igbo-Ukwu, Jihar Anambra a ranar 20 ga Nuwamba 1937. Bai halarci makarantar sakandare ba, amma ya koyar da kanshi ta hanyar karantarwa, inda ya cancanci shiga jami’a. Ya sami digiri na BSc a fannin tattalin arziki a Jami’ar Badun, sannan ya halarci Jami’ar Harvard inda ya samu gurbin karatu na gidauniyar Rockefeller inda ya sami digiri na biyu sannan ya yi digiri na uku a shekarar 1972. Ya zama shugaban makaranta, malami a Kwalejin Jami’ar Makarare da ke Kampala, Uganda. Malamin Koyarwa a Jami’ar Harvard, kuma mai ba da shawara tare da Arthur D. Little a Cambridge, Massachusetts. Ezeife ya shiga aikin farar hula ne a matsayin jami’in gudanarwa kuma ya kai matsayin Sakatare na dindindin.

 

Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa kuma tsohon dan takarar shugaban kasa.

 

 

“Wannan abin bakin ciki ya faru ne jiya da karfe 6 na yamma a babban asibitin tarayya dake Abuja. Daga baya za a bayyana karin bayani game da marigayin da kuma yadda za a yi jana’izar sa,” in ji sanarwar.

 

Mutuwar Ezeife na zuwa ne bayan watanni ashirin da rasuwar matarsa, kuma watanni takwas bayan wani tsohon gwamnan jihar, Cif Chinwoke Mbadinuju shi ma ya shiga cikin kakanninsa.

 

 

Dr. Ezeife wanda aka fi sani da Okwadike Igboukwu, an zabe shi gwamnan jihar Anambra daga watan Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993 a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.