Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Zaman Makokin Tsohon Gwamnan Jihar Anambara Cif Ezeife

242

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar tsohon gwamnan jihar Anambara Cif Chuwkuemeka Ezeife a matsayin rashi mai raɗaɗi.

 

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Ajuri Ngelale ,Shugaban ya jajantawa iyalan Ezeife, jama’a, da gwamnatin jihar Anambara.

 

 

Da yake jinjinawa irin gudunmawar da Cif Ezeife ya bayar ga ci gaban kasa, Shugaban na Najeriya ya tuno da irin tasirin da tsohon gwamnan ya yi wajen tsara maganganun jama’a da gudanar da mulki a Najeriya, da kuma harsashin da ya shimfida domin ci gaban jihar Anambra.

 

 

Shugaba Tinubu ya kuma amince da irin nasarorin da tsohon sakataren din-din-din na gwamnatin tarayya ya samu a fagen siyasar Najeriya da kuma irin yadda ya jagoranci kasar.

 

 

A yayin da yake addu’ar Allah ya jikan marigayin, shugaban ya karfafawa masoyansa gwiwa da su yi ta’aziyyar gadon da ba a taba mantawa da shi ba.

 

 

 

An haifi Chukwuemeka Ezeife a ranar 20 ga watan Nuwamba 1937.

 

 

Ya kasance dan siyasar Najeriya wanda yayi gwamnan jihar Anambra daga watan Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993 a lokacin jamhuriya ta uku ta Najeriya.

 

 

Cif Ezeife wanda ya bayyana kansa a matsayin mai bin tafarkin dimokuradiyya, a rayuwarsa an nada shi mai baiwa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawara kan harkokin siyasa.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.