Take a fresh look at your lifestyle.

Ukraine: Kyiv Ta Ce Ta Yi Nasara kan Harin Da Jiragen Saman Rasha Suka kai

105

Jami’an sojin Ukraine sun ce da sanyin safiyar Larabar nan ne kasar Rasha ta kaddamar da harin ta sama karo na biyar inda ta auna Kyiv tare da lalata na’urorin tsaron sama da jiragen sama marasa matuka da ke tunkarar babban birnin kasar.

 

Rundunar sojin saman Ukraine ta ce tsarin tsaron sama ya lalata jiragen sama marasa matuka guda 18 cikin 19 da aka harba a Kyiv, Odesa, Kherson da sauran yankuna na Ukraine. Har yanzu dai ba a bayyana ko nawa ne aka lalata ba a birnin Kyiv.

 

“A cewar bayanan farko, ba a sami asarar rai ko barna a babban birnin ba,” in ji Serhiy Popko, Shugaban Hukumar Soja ta Kyiv a cikin manhajar aika saƙon Telegram.

 

Rundunar sojin saman Ukraine ta kuma ce Rasha ta kai hari a yankin Kharkiv da ke gabas da makami mai linzami guda biyu da ke kan hanya zuwa sama. Ya kara da cewa, ba a samu asarar rai ba sakamakon harin.

 

Babu wani karin haske daga Rasha.

 

Rasha ta fara kai hare-hare kan makamashi, soji da kayayyakin sufuri na Ukraine a yankuna da ke da nisa daga fagen daga a watan Oktoban 2022, watanni shida bayan da sojojin Moscow suka gaza kwace Kyiv tare da ficewa zuwa Gabas da Kudu na Ukraine.

 

Yawancin kudu maso gabashin Ukraine sun kasance a karkashin sanarwar hare-hare ta sama da karfe 2300 agogon GMT, inda sojojin saman Ukraine suka ce yankunan Kharkiv, Dnipropetrovsk da Kirovohrad na fuskantar barazanar hare-haren makamai masu linzami na Rasha.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.