Malesiya ta haramtawa dukkanin jiragen dakon kaya masu dauke da tutar Isra’ila sauka a tashar jiragen ruwan ta a wani mataki da ta ce martani ne ga yakin Gaza, tana mai zargin Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa ta hanyar “kisa da zaluncin da ake yi wa Falasdinawa”.
A ranar Laraba ne firaministan kasar Malaysia Anwar Ibrahim ya sanar da matakin kakaba dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa da ke da alaka da kasar Isra’ila, inda ya kebanta da kamfanin ZIM, babban kamfanin jigilar kayayyaki na kasar Isra’ila, a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna fargaba kan katsewar jiragen ruwa a duniya, sakamakon hare-haren da aka kai kan jiragen ruwan dakon kaya a tekun Bahar Maliya. .
Anwar ya ce, za a kuma hana jiragen da ke kan hanyarsu ta zuwa Isra’ila lodin kaya a kowace tashar jiragen ruwa a yankin kudu maso gabashin Asiya nan take.
Malesiya, wacce kusan kashi 60 na al’ummar musulmi ne, ba ta kulla huldar diflomasiyya da Isra’ila, tana kuma ra’ayin samar da kasashe biyu na warware rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Anwar ya ce “Gwamnatin Malaysia ta yanke shawarar toshewa tare da hana kamfanin jigilar kayayyaki na Isra’ila ZIM daga tashar jiragen ruwa na Malaysia.”
Hane-hane martani ne “ga ayyukan Isra’ila da suka yi watsi da ka’idojin jin kai na asali da kuma keta dokokin kasa da kasa ta hanyar kisan kiyashi da rashin tausayi ga Falasdinawa”.
Malaysia “kuma ta yanke shawarar daina karbar jiragen ruwa masu amfani da tutar Isra’ila don shiga cikin kasar” tare da hana “duk wani jirgi da ke kan hanyarsa ta zuwa Isra’ila daga lodin kaya a tashar jiragen ruwa na Malaysia”.
“Dukkan waɗannan hane-hane suna aiki nan da nan,” in ji Firayim Minista.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.