Take a fresh look at your lifestyle.

Gaza: Amurka Ta Nuna Goyon Bayan Ta Ga kudurin Ba Da Agaji Na Majalisar Dinkin Duniya

111

Amurka ta nuna goyon bayan ta ga sabon daftarin kudurin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi kan taimakon jin kai ga Gaza a yau ake sa ran kada kuri’a.

 

Daftarin asali ya yi kira da a dakatar da tashe-tashen hankula masu dorewa, amma sigar karshe ta yi kira da a samar da yanayin daya.

 

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hukumar Abinci ta Duniya ta ce Gaza na fuskantar barazanar yunwa a cikin watanni shida idan rikicin bai kawo karshe ba

 

A halin da ake ciki, Hamas ta ce kungiyoyin Falasdinawa sun yi watsi da batun sake sakin mutanen da aka yi garkuwa da su har sai Isra’ila ta amince da kawo karshen yakin Gaza.

 

Amma Isra’ila ta sha yin watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta na dindindin, inda ministan tsaron kasar ya ce kawo karshen yakin kafin a ci nasara da Hamas zai zama ” gazawa”.

 

Ana ci gaba da tattaunawa a birnin Alkahira kan cimma wata sabuwar yarjejeniya a yakin.

 

A ranar Laraba, gwamnatin Gaza ta ce mutane 20,000 aka kashe a can tun bayan da Isra’ila ta kaddamar da yakinta na yaki da kungiyar.

 

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.