Take a fresh look at your lifestyle.

Cire Jinjiri Ta Hanyar CS Ba Illa Ne Ba : Dr Abubakar

Shehu Salman, Sokoto

228

Kimanin mata dubu daya da arba’in da bakwai cikin dubu dari ne ke rasa rayukansu yayin haihuwa a Najeriya, gwamnatin kasar hadin gwuiwa da kungiyoyi masu zaman kasu sun yunkuro domin rage yawan mace-macen da kasa da kaso saba’in cikin dubu dari nan da shekara ta 2030.

Wata kungiya da ke bayar da agajin kiwon lafiya ta MOMENTUM safe surgery a jihar Sokoto arewa maso yammacin kasar ta gudanar da bincike ta yadda za’a ceto rayuwar iyaye mata kamar yadda yake a ko ina na faɗin duniya.

Binciken ya gano cewa ta hanyar yi wa mata masu matsala aiki ne wato CS kadai za a iya shawo kan mace-macen mata masu juna biyu yayin haihuwa. A bisa haka ne ƙungiyar ta Momentum ta gudanar da bincike dangane da abinda ke kawo fargaba ga al’umma. Dr. Abubakar Danladi shine ya gudanar da binciken.
“Abinda muka gano shine, ana samun matsalar tsangwama da rashin cikakken bayanin yadda aikin CS ɗin yake daga bangaren jami’an kiwon lafiya, wanda ta haka ne za a fidda tsoro a zukatan masu juna biyu da danginsu”. In ji Dr. Abubkar

Mata na da damar neman bayanai dangane da yadda za ayi masu CS da yadda aikin yake da kuma ƙarin bayani bayanin yadda aka gudanar da CS ɗin bayan an kammala. Alhaji Sani Umar Jabbi basarake ne da ke magantuwa kan ababen da suka jiɓanci tsarin iyali.

“Wayar wa al’umma da kai game da haihuwa ta hanyar CS zai taimaka matuƙa wajen rage duk wata jita-jita kan illar CS”. A cewar Alhaji Sani

A wasu ƙasashen da suka ci gaba, mata kan zaɓi haihuwa ta CS a bisa raɗin kasu a matsayin hanyar da zasu rabu da juna biyun da ke tare dasu.

Abdulkarim Rabiu

Comments are closed.