A wani bangare na shirye-shiryen da ake yi na yiwuwar kamuwa da cutar zazzabin Lassa, Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC), Dakta Ifedayo Adetifa ya kai wata muhimmiyar ziyara a jihar Bauchi kwanan nan.
KU KARANTA KUMA: NCDC, masu ruwa da tsaki sun yi hadin gwiwa kan shirin Bincike na Zazzabin Lassa na shekara 5
Dokta Adetifa ya ce makasudin ziyarar ita ce karfafa matakan da jihar ke dauka kan barkewar cutar tare da tabbatar da ingantaccen shiri.
Jihar Bauchi ta kasance abin damuwa tun daga shekarar 2022, inda ta kasance a matsayi na daya a cikin jihohi uku da suka fi yawan masu kamuwa da zazzabin Lassa.
“A shekarar 2023 kadai, jihar ta samu mutane 945 da ake zargi da kamuwa da cutar, yayin da 160 aka tabbatar da kamuwa da cutar sannan 33 sun mutu. Gaggawar lamarin ya sa aka kai ziyarar ban girma ga manyan cibiyoyin kiwon lafiya a jihar,” inji shi.
A yayin ziyarar tasa, Dokta Adetifa ya tattauna da kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya, da kananan hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki domin tantance halin da ake ciki na shirye-shiryen da kuma gano wuraren da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.
Ya kara da cewa, “yunkurin hadin gwiwa na da nufin karfafa tsarin kiwon lafiya na Bauchi, da inganta matakan sa ido, da kuma karfafa karfin sarrafawa da shawo kan barkewar cutar zazzabin Lassa,” in ji shi.
Darakta Janar na NCDC ya bayyana kudurin bayar da tallafin da ya dace, wadanda suka hada da kayayyakin jinya, da ma’aikata, da taimakon fasaha don tabbatar da daukar matakan da suka dace kan karuwar masu kamuwa da cutar a Bauchi.
“Wannan ziyarar ta jaddada sadaukarwar da NCDC ta yi na dakile yaduwar cututtuka da kuma kare lafiya da jin dadin al’ummar Najeriya,” in ji shi.
Dangane da ziyarar Dr. Adetifa, hukumomin kiwon lafiya na jihar Bauchi sun kara kaimi wajen aiwatar da matakan kariya, gudanar da gangamin wayar da kan jama’a, da inganta cudanya da jama’a.
Mahukuntan jihar Bauchi sun ce, “Hanyar hadin gwiwa tsakanin hukumar NCDC da jihar shaida ce ta sahihan matakan da ake dauka wajen magance matsalolin kiwon lafiyar jama’a, wanda ke nuna muhimmancin hada karfi da karfe wajen yaki da cututtuka masu yaduwa.”
Ladan Nasidi.