Akalla Falasdinawa 70 ne aka kashe a wani hari ta sama da aka kai a sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi, wanda kakakin ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ya bayyana a matsayin kisan kiyashi.
Sojojin Isra’ila sun yarda cewa suna fada da “rikitaccen yaki” tare da kashe sojoji da yawa. Ta ce an tsinto gawarwakin mutane akalla biyar da aka yi garkuwa da su daga wani rami a arewacin Gaza.
Fiye da Falasdinawa 20,400 ne aka kashe a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba. Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da Hamas ta kai Isra’ila ya kai 1,139.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.