Majalisar Wakilai Ta Bukaci Bincike Kan Kisan Gillar Da Dan China Ya Yi Wa Wata ‘yar Najeriya.
Abdulkarim Rabiu, Abuja
Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba da ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan mumunan kisan da wani dan kasar China, Mista Geng Quanrong ya yi wa Ummulkulthum Buhari a Jihar Kano dake Arewa maso yammacin Najeriya.
Majalisar ta kuma bukaci jakadan kasar Sin dake Najeriya da jama’ar kasar Sin dake jihar Kano da su jajantawa gwamnati da jama’ar jihar Kano da ma Najeriya baki daya.
Hakan ya biyo bayan wani kudiri dake bukatar daukar matakin gaggawa wanda dan majalisa daga jihar Kano, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya dauki nauyi.
Da yake jagorantar muhawarar, Hon. Alhassan, ya bayyana damuwarsa kan yadda Mista Geng ya dauki sama da sa’a guda kafin ya kutsa kansa shiga dakin marigayin wanda hakan ya nuna cewa harin da kisan da aka yi wa marigayiyar shiri ne da aka yi na aikata laifin da gangan.
‘Dan majalisar ya ce mutuwarta ba kawai ta yi wa ‘yan uwanta illa ba, har ma da al’ummar jihar Kano da ma Nijeriya baki daya.
Bayan wata kwakkwarar muhawara kan kudurin, yawancin ‘yan majalisun sun amince da shawarari da aka bayar ta hanyar kada kuri’a.
Majalisar ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin cikin gida da ya ziyarci tare da jajantawa iyalan mamacin da jama’a da gwamnatin jihar Kano.
Majalisar ta kuma bukaci hukumomin da abin ya shafa da su dakatar da ayyukan kamfanin da dan kasar Chanan ke aiki har sai an tantance matsayin mutumin da ake tuhuma da aikatan laifin.
Abdulkarim
Leave a Reply