Tsohon kakakin majalisar wakilai, Honorabul Ghali Umar Na’Abba ya rasu
Mai magana da yawun Majalisar Wakilai a Najeriya ta 4 ya rasu a asibitin kasa dake Abuja da misalin karfe 3 na safiyar Laraba.
An haifi Na’Abba ranar 27 ga Satumba, 1958 a Tudun Wada, jihar Kano.
Ya taba zama kakakin majalisar wakilai, kuma dan jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), daga 1999 zuwa 2003.
Yana da shekaru 65.
Ladan Nasidi.