Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ce Sojojin Isra’ila ba za su rage karfin fada ba kuma suna “zurfafa ayyukan su a Kudancin Gaza”, tare da kai hari kan 100 a cikin sa’o’i 24.
Babban Sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nada Sigrid Kaag a matsayin mai kula da ayyukan agaji na Gaza, amma hanyar da ke gaban kai agajin jin kai na da wahala ba tare da fasa fada ba.
Herzi Halevi, Babban Hafsan Sojojin Isra’ila, ya ce yakin Gaza zai ci gaba da “watanni da yawa”.
A Gaza, akalla mutane 20,915 aka kashe tare da raunata 54,918 a hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga watan Oktoba. Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da Hamas ta kai Isra’ila ya kai 1,139.
ALJAZEERA/Ladan Nasidi.