Take a fresh look at your lifestyle.

Soja: Rasha Da Indiya Sun Yi Shirin Samar Da Kayan Aikin Soji Tare

112

Rasha da Indiya sun samu ci gaba mai ma’ana a tattaunawar da suka yi kan shirin samar da kayan aikin soji tare, in ji ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a ranar Laraba bayan tattaunawa da takwaran shi na Indiya Subrahmanyam Jaishankar a birnin Masko.

 

Da yake magana a wani taron manema labarai, Lavrov ya ce irin wannan hadin gwiwa na da dabara mai kyau kuma yana da moriyar kasashen biyu kuma zai taimaka wajen tabbatar da tsaro a nahiyar Eurasia.

 

Ya ce Moscow ta mutunta sha’awar Indiya na samar da kayan aikin soja kuma a shirye take ita ma ta goyi bayan sha’awar New Delhi na kera abubuwan da Indiya ke bukata a Indiya.

 

Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin zai gana da Jaishankar nan gaba a ranar Laraba.

 

Jaishankar ya ce yana sa ran Putin da Firayim Ministan Indiya Narendra Modi za su gana a shekara mai zuwa.

 

Jaishankar ya ce, shi da Lavrov sun tattauna kan rikice-rikicen da ke faruwa a Ukraine da Gaza, da kuma harkokin kasuwanci da zuba jari.

 

Indiya ta zama daya daga cikin manyan abokan tattalin arzikin Rasha tun bayan da kasashen yamma a cikin 2022 suka kakaba wa Moscow takunkumi mai tsauri kan yakin Ukraine.

 

Rasha ta karkatar da yawancin man da take fitarwa zuwa Indiya tare da kara kaimi a fannin diflomasiyya a cikin kungiyar kasashen BRICS, kungiyar da kasashen biyu ke cikin ta.

 

A cewar Jaishankar, ana sa ran cinikin Indiya da Rasha zai kai dala biliyan 50 a bana.

 

Ya ce, New Delhi na sha’awar sanya hannu kan yarjejeniyar zuba jari tsakanin kasashen biyu da Rasha, da kuma yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci da kungiyar tattalin arzikin Eurasia karkashin jagorancin Masko.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.