Masar ta tabbatar da cewa ta gabatar da wani tsari na kawo karshen rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Hamas a zirin Gaza wanda ya kunshi matakai uku da ke kawo karshen tsagaita bude wuta, ta kuma ce tana jiran martani kan shirin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, shugabar ma’aikatar yada labarai ta Masar Diaa Rashwan ta ce Masar za ta ba da cikakkun bayanai kan shirin da zarar an samu wadannan martani.
Shawarar wani yunƙuri ne na “ƙusa ra’ayi tsakanin dukkan bangarorin da abin ya shafa, a ƙoƙarin dakatar da zubar da jinin Falasɗinawa da ta’addanci a zirin Gaza da maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,” in ji shi.
A baya majiyoyin tsaron Masar sun ce shawarar ta hada da tsagaita bude wuta mai matakai da dama da ya shafi sakin fursunonin Isra’ila da Hamas.
Wata majiyar Masar ta ce an taso da manufar kafa gwamnatin Gaza bayan yakin.
Reuters/Ladan Nasidi.