Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2024 na Naira tiriliyan 28.78 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Shugaba Tinubu, wanda ya isa ofishin sa daga filin jirgin sama da misalin karfe biyu na rana, kai tsaye ya nufi wurin bikin sanya hannu a kan kasafin kudin.
Sauran wadanda ke tare da Shugaban kasar yayin da ya rattaba hannu a kan kasafin sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas.
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun; Ministan Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki, Alhaji Atiku Abubakar; Shi ma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ya kasance a wajen.
Haka kuma akwai; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Hon Femi Gbajabiamila; Shugaban jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje; Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Sanata Olamilekan Adeola da dai sauransu.
Ladan Nasidi.