Take a fresh look at your lifestyle.

Beirut: Ana Fargabar Tashin Hankali Bayan Kashe Wani Babban Jami’in Hamas

107

An kashe babban jami’in Hamas Saleh al-Arouri a wani hari da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin Beirut na kasar Lebanon. Isra’ila ba ta dauki alhakinta a hukumance ba.

 

Hezbollah ta ce harin, wanda ya kashe akalla mutane shida, “ba zai wuce ba tare da hukunci ba”.

 

Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce harin da Isra’ila ta kai a asibitin garin El Amal da ke Khan Younis a Kudancin Gaza ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla biyar.

 

Akalla mutane 22,185 ne suka mutu yayin da wasu 57,000 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin na ranar 7 ga watan Oktoba a Isra’ila ya kai 1,139.

 

 

 

ALJAZEERA/ Ladan Nasidi.

Comments are closed.