Dan wasan Super Eagles na Najeriya, Sunusi Ibrahim ya dauki nauyin mutane 110 da suka ci gajiyar hukumar inshorar lafiya ta jihar Nasarawa (NASHIA) na tsawon shekara daya ta hanyar gidauniyar shi ta SI14.
Ibrahim ya raba katin shaida na NASHIA domin samun damar gudanar da ayyukan kiwon lafiya kyauta ga wadanda suka amfana a karamar hukumar Keffi a ranar Talata.
KU KARANTA KUMA: Hukumar inshorar lafiya ta Nasarawa za ta yi wa masu rajista 500,000 nan da 2027
Da yake zantawa da manema labarai, Ibrahim ya ce an yi hakan ne domin a rage wahalhalun da wasu jama’a ke fuskanta ta fuskar samun saukin isar da kiwon lafiya.
Ya ce mutanen 110 da suka ci gajiyar tallafin sun hada da tsofaffi, da masu bukata ta musamman, yara ‘yan kasa da shekaru biyar, mata masu juna biyu, zawarawa, da kuma marasa galihu da ke garin Keffi.
“Na yi wannan kokarin ne domin na san halin da wasu mutanen kasar ke ciki na da wahala. Shi ya sa ke da wuya su je asibiti domin samun muhimman bukatu na kiwon lafiya.
“Saboda haka na yi tunani sosai game da hakan kuma na yanke shawarar tallafa mu su ta hanyar daukar nauyin shigar su Hukumar Inshorar Lafiya ta Jihar Nasarawa,” inji shi.
Ibrahim ya ce zai ci gaba da hada kai da hukumar domin wayar da kan al’ummar garin Keffi kan muhimmancin inshorar lafiya da kuma kara samun damar shiga tsarin.
“Lokacin da suka zo wurina suka ba da shawarar, na amince da shi da zuciya ɗaya domin ra’ayi ne mai ban sha’awa kuma hanya ce mai kyau na mayar da hankali ga al’umma,” in ji shi.
Dan wasan ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi da kuma ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su goyi bayan wannan yunkurin ta hanyar samun karin mazauna yankin.
Shima da yake nasa jawabin, babban sakataren hukumar NASHIA, Dakta Yahaya Ubam, ya yabawa dan wasan bisa wannan karimcin, musamman wajen samar da masu karamin karfi.
“Na yi matukar farin ciki da wannan ci gaban. Maimakon mutane su jefar da kuɗi ba tare da sarrafa su yadda ya kamata ba, ya yanke shawarar yin tasiri ga rayuwar al’ummar shi.
“Kashe kudi daga aljihun ku yana da babban jari, musamman a Najeriya a yau, domin duk mun san abin da ke faruwa.
“Ba da kaɗan don kula da lafiyar wasu babban abin alfahari ne. Don haka muna gode masa kuma za mu ci gaba da hada kai da shi da sauran ’yan Najeriya masu kishin kasa domin samun wasu da dama da shirin ya shafa,” inji shi.
Nwosu Benedict, wanda ya ci gajiyar tallafin, ya ce idan da yawan ‘yan Najeriya za su iya yin koyi da matakan da dan wasan ya dauka, kasar za ta fi kyau.
“Na yi farin cikin kasancewa a nan. Ba batun fesa kudi nan da can ba. Abin da matashin ya yi zai taimaka matuka wajen taimaka wa wasu daga cikin mu su samu ayyukan kiwon lafiya,” inji shi
NAN/Ladan Nasidi.