Take a fresh look at your lifestyle.

Rasha Ta Kai Wa Yankin Yukrain Hari Da Makami Mai Linzami Da Ba Na Rasha Ba

160

Rasha ta kai hari a yankin Kharkiv na gabashin Yukrain da makamai masu linzami da ba na Rasha ba, in ji gwamnan yankin a ranar Juma’a.

 

Bayanin na Oleh Synehubov, wanda kamfanin yada labarai na kasar Ukraine Suspilne ya ruwaito, ya biyo bayan ikirarin da Amurka ta yi a ranar Alhamis cewa, a baya-bayan nan Rasha ta yi amfani da makamai masu linzami masu cin gajeren zango (SRBMs) da ta samo daga Koriya ta Arewa, wajen kai hare-hare da dama kan Ukraine.

 

“Muna gudanar da dukkan gwaje-gwajen da suka dace. Zan ce a yanzu an goge alamun daga wadannan makamai masu linzami, amma abin da muke iya gani (shi ne) kasar da ta samar da ita ba Tarayyar Rasha ba ce, ”in ji Suspilne Synehubov.

 

Ukraine ba ta tabbatar da ikirarin da Amurka ta yi cewa makamin na Koriya ta Arewa ba ne. Kakakin rundunar sojin saman Ukraine ya fada da safiyar Juma’a cewa har yanzu Kyiv bai samu labarin ko makaman na Koriya ta Arewa ba ne.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.