Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirin inganta asibitin kasusuwa na Gen. Amadi Rimi zuwa matsayin cibiyar kula da lafiya.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Soludo ya kaddamar da sabon asibiti a jihar Anambara
Gwamna Dikko Radda ya bayyana hakan ne a Katsina a ranar Juma’a, a lokacin da mahukunta da kuma wadanda suka kafa Jami’ar Al-Qalam Katsina, karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami’ar Farfesa Nasir Yahaya-Daura suka kai masa ziyarar ban girma.
Radda ya ce, kwamitin kwararrun likitocin ya dauki nauyin bayar da shawarwarin da suka dace don inganta aikin tare da ci gaba da aikin gina cibiyar dialysis a asibitin.
Ya ce, “Akwai ci gaba da tattaunawa da Saudiyya da sauran kasashen ketare domin zuba jari a fannin kiwon lafiya a jihar.
“Manufar ita ce inganta ayyukan kiwon lafiya sosai.”
Ya kara jaddada kudirin shirin na rage bukatuwar jinya a kasashen waje, da amfanar jama’ar Katsina da makwabta.
Radda ya ce gwamnatin jihar tana kuma tuntubar wasu masu ba da shawara daga Tokyo da Burtaniya (Birtaniya), don hadin gwiwar gudanar da cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.
“Yadda za a iya inganta asibitin shi ne ya zama asibitin koyarwa na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da sauran jami’o’in jihar da zarar yarjejeniyar shekaru 15 ta kare da Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya.”
Gwamnan ya karfafa gwiwar mahukuntan Jami’ar Al-Qalam da su nemi a saka su cikin ayyukan Tetfund daga gwamnatin tarayya, inda ya ba su tabbacin goyon bayan shi.
A nasa bangaren, Yahaya-Daura ya nuna jin dadinsa da jajircewar gwamnan tare da neman a tallafa wa jami’ar katanga saboda matsalolin tsaro.
Ladan Nasidi