Take a fresh look at your lifestyle.

Najeriya Na Binciken Zargin Amfani Da Kudade Da Ma’aikatar Jin Kai Ta Yi

99

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Najeriya na gudanar da bincike a kan zargin da ma’aikatar kula da jin kai da yaki da fatara ta yi na biyan kudaden gwamnati a wani asusu na sirri.

 

“Shugaban kasa ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da daidaito da ingancin bayanan da aka ruwaito,” Mohammed Idris ya ce a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi 7 ga Janairu, 2024.

 

KU KARANTA KUMA: Tsohon Minista bata yi watsi da gayyata ba – EFCC

 

Ministan ya ce gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana, kuma za ta tabbatar da an gano duk wani abu da ya saba wa doka da kuma hukunta shi.

 

Sanarwar ta zo ne a daidai lokacin da ake yada rahotanni a kafafen sada zumunta da na yanar gizo cewa ma’aikatar jin kai da ke kula da rabon kayan agaji da walwala ga miliyoyin ‘yan Najeriya, ta tura kudade zuwa wani asusu mai alaka da wani mutum mai zaman kansa.

 

Idris ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri yayin da ake gudanar da bincike, kuma su dogara da ma’aikatar a matsayin babbar hanyar samun ingantattun bayanai.

 

Ya yi gargadi game da “labarai daban-daban da ba a tantance su ba da ke yawo a yanar gizo,Intanet” wadanda za su iya yaudarar jama’a.

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa da kuma inganta harkokin mulki a kasar da ta fi kowace kasa yawan jama’a kuma mafi karfin tattalin arziki a Afirka.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.