Wasu ‘yan bindiga sanye da takunkumin rufe fuska sun kutsa kai tsaye a gidan talabijin a Ecuador tare da tsoratar da ma’aikatansu.
An tilasta wa ma’aikata sauka a kasa yayin watsa shirye-shiryen ta gidan talabijin na jama’a TC a cikin birnin Guayaquil kafin a tsinke sadarwar kai tsaye.
‘Yan sandan sun ce daga baya sun sako dukkan ma’aikatan da aka yi garkuwa da su tare da kama mutane 13, tare da nuna makaman da aka kwato.
Akalla mutane 10 ne suka mutu tun bayan kafa dokar ta-baci ta kwanaki 60 a Ecuador ranar Litinin.
An ayyana dokar ta-baci ne bayan da wani dan daba da ya yi kaurin suna ya bace daga gidan yari. Babu tabbas ko lamarin da ya faru a gidan talabijin na Guayaquil yana da nasaba da bacewar mutumin daga gidan yari a wannan birni na shugaban kungiyar Choneros, Adolfo Macías Villamar, kamar yadda aka fi sani da shi.
A makwabciyar kasar Peru, gwamnatin kasar ta ba da umarnin tura jami’an ‘yan sanda cikin gaggawa zuwa kan iyaka domin hana duk wani tashin hankali da ya shiga kasar.
Amurka ta ce ta yi Allah-wadai da harin ta’addancin da aka kai a Ecuador kuma tana “hadin gwiwa” tare da Shugaba Daniel Noboa da gwamnatin shi ta Ecuador kuma a shirye take domin ba da taimako.
Ecuador tana daya daga cikin manyan masu fitar da ayaba a duniya, amma kuma tana fitar da mai, kofi, koko, jatan lande da kayayyakin ruwa. Ana danganta karuwar tashe-tashen hankula a kasar Andean, ciki da wajen gidajen yarin ta, da fada tsakanin masu safarar miyagun kwayoyi, na kasashen waje da na cikin gida, kan sarrafa hanyoyin da hodar iblis ta kai Amurka da Turai.
Ana iya jin wata mata tana roƙon, “Kada ku yi harbi, don Allah kar ku yi harbi,” in ji kamfanin dillancin labarai na AFP, yayin da ake jin wani mutum yana kururuwa da alamun zafi.
“Dama sun shigo ne domin su kashe mu,” wani ma’aikacin TC ya shaida wa AFP a cikin sakon WhatsApp. “Don Allah kada wannan ya faru. Masu laifin suna kan iska.”
Shugaba Noboa ya ce yanzu haka akwai “rikicin cikin gida” a kasar kuma yana tara sojojin kasar don aiwatar da “ayyukan soji domin kawar da su” abin da ya kira “manyan laifuffuka na kasa da kasa, kungiyoyin ‘yan ta’adda da masu fafutuka da ba na gwamnati ba”.
Ya na mai da martani ne kan tarzomar gidan yari da kuma tserewa daga gidajen yari da sauran tashe-tashen hankula da hukumomi ke zargi
ƙungiyoyin masu laifi.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, an yi garkuwa da akalla jami’an ‘yan sanda bakwai, kuma wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna uku daga cikin jami’an da aka sace zaune a kasa tare da nuna musu bindiga yayin da aka tilasta wa daya ya karanta wata sanarwa da aka aika wa shugaba Noboa.
‘Yan sanda sun ba da umarnin ficewa daga harabar gwamnati da ke Quito saboda matsalar tsaro.
Mazauna Quito sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa birnin na cikin rudani tun bayan labarin harin da aka kai a gidan talabijin na Guayaquil.
“Akwai fargaba da yawa a cikin birnin,” in ji Mario Urena. “A wurin aiki, mutane suna suna ficewa da wuri. Duk mutanen suna tafiya, ga kuma cunkoso da ƙararrawa a ko’ina saboda hargitsi.”
Wasu mutane a birnin Cuenca sun shaida wa AFP kaduwarsu da ganin an kama gidan talabijin din.
Francisco Rosas ya ce “A Ecuador, ba mu taba ganin irin wannan abu ba, inda kusan an sace wata tasha kuma ana fara watsa shirye-shirye da harbe-harbe, tare da yin garkuwa da mutane,” in ji Francisco Rosas. “To wane irin hali muke ciki na tsaro? Kuma idan gidan talabijin zai iya samun irin wannan nau’in fashi, irin wannan rashin tsaro, tunanin gidajen abinci ko shaguna.”
BBC/Ladan Nasidi.