Take a fresh look at your lifestyle.

‘Yan Jarida 11 Sun Samu Horo A Kaduna

109

An horar da ’yan jarida mata 11 tare da wasu zababbun mata a jihar Kaduna a kan harshen Hausa a cikin shirin wiki na son mata.

Shugabar wiki-media ce ta shirya shirin, wanda Bashir Yahuza Mohammed, jami’in yada labaran wiki na Arewacin Najeriya ne ya shirya shi.

Da yake zantawa da manema labarai a wajen taron a Kaduna, Bashir Yahuza Muhammad ya bayyana cewa, horon na da nufin ilmantar da matan kan yadda za su kara zage damtse ta hanyar wiki-media, dandalin sada zumunta.

A cewarsa, ICT na daya daga cikin hanyoyin sadarwa da mu’amala cikin sauri, don haka akwai bukatar mata musamman na arewa su kara kaimi.

A nata bangaren, mai wayar da kan mata, sakatariyar kungiyar NAWOJ ta shiyyar A, Daharatu Ahmed Aliyu ta bayyana cewa horon ya dace domin matan arewa na bukatar ganin sun dace da yanayin zamani a duniya.

A wata tattaunawa ta daban, wasu mahalarta taron da suka hada da shugabar kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kaduna, Kwamared Fatima Aliyu Mahuta da ko’odineta Kaduna arewa jam’iyyar matan Arewa, Fatima Ahmed Godowoli sun yabawa wadanda suka shirya taron tare da yin alkawarin fadada ilimin da suka samu kungiyoyin su na mata.

Mahalarta taron sun fito ne daga Kungiyar Matan Jarida ta Najeriya – NAWOJ, National Council of women Society- NCWS, Jam’ iyya Matan Arewa, Dandalin Matan Siyasa da dai sauransu.

 

Comments are closed.