Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Sin Ta Yi Kira Sa A Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Na Gaza

88

 

Kasar Sin ta yi kira da a gudanar da wani babban taro mai iko kan yakin Gaza.

 

Da yake jawabi a kasar Masar a karshen mako, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira da “tsara wani takamaiman jadawalin lokaci da taswirar hanya domin aiwatar da “matsayin kasashe biyu” da goyon baya ga sake dawo da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasdinu cikin gaggawa.

 

Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce kusan mutane 24,000 ne suka mutu a harin da Isra’ila ta kai tare da jikkata sama da 60,000.

 

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta koma wani sabon salo na yakin da aka mayar da hankali kan kudancin Gaza, inda a yanzu haka kusan mutane miliyan 2 ke mafaka a cikin tantuna da wasu matsuguni na wucin gadi, bayan da matakin farko ya ta’allaka ne kan kawar da arewacin gabar tekun , ciki har da birnin Gaza.

 

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya yi watsi da kiraye-kirayen tsagaita wuta, yana mai cewa Isra’ila za ta ci gaba da tafiya har sai ta samu cikakkiyar nasara kan Hamas tare da kwato sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.