Dakarun Bataliya ta 192, Division 81, sojojin Najeriya sun kama wani da ake zargin kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ne da ke dauke da haramtattun abubuwa, wadanda ake zargin tabar wiwi ce ta Cannabis Sativa.
KU KARANTA KUMA: Sojojin Najeriya sun kashe mutane 86, sun kama ‘yan ta’adda 101
Dakarun da ke aiki da sahihan bayanan sirri sun kama wadanda ake zargin suna aiki da wata mota kirar Sienna 2001 Model Space Bus, mai lamba Legas APP 129 EF, a ranar Lahadi 14 ga watan Janairu, 2024, a kan iyakar Balogun a jihar Ogun.
Sanarwar da Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce, dakarun ‘yan banga sun gudanar da bincike sosai kan motar tare da gano wasu dakunan da ke cike da abunda ake zargin tabar wiwi ce guda 296 .
Sanarwar ta ci gaba da cewa, binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa an yi jigilar haramtattun kayan ne daga jamhuriyar Benin, ta kan iyakar Ilara a kan hanyar Ifo a jihar Ogun.
Wani bincike da aka yi alao ya nuna cewa, sai da masu safarar miyagun kwayoyi na kasashen ketare suka kwashe watanni biyar kafin su boye abun domin kai wa abokan huldarsu. An kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifin.
Wadanda ake zargin sun hada da Mista Adigun Olatunji mai shekaru 54 da kuma Mista Michael Atanda mai shekaru 18, dukkansu daga Ilara Imeko a karamar hukumar Afun ta jihar Ogun, suna zaune ne a jamhuriyar Benin. An kai su gidan yari domin kara daukar matakan da suka dace, bayan yunkurin bai wa sojoji cin hancin Naira miliyan goma sha biyu (12,000,000.00).
Sauran kayayyakin da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da katin shaidar dan kasa na jamhuriyar Benin daya, katin dan Najeriya daya da kuma kananan wayoyin Itel guda biyu. Sauran sun hada da lasisin tuki na Jamhuriyar Benin daya, Fasfo na kasa da kasa na Jamhuriyar Benin, fakitin SIM guda shida na Jamhuriyar Benin, katin SIM na Jamhuriyar Benin 2, lasisin tuki na Najeriya daya, naurar samar da cajin wayar salula daya da na’urar MP3 guda daya.
Bugu da kari, an kwato katin ma’adanar ajiya, da laya na gida, da kuma kudi dubu hamsin da biyu, da naira dari bakwai (52,700.00) kawai daga hannun wadanda ake zargin.
Wadanda ake zargin da dukkan kayayyakin da aka kwato suna tsare har zuwa lokacin da za a mika su ga hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa domin gurfanar da su gaban kuliya.
Idan dai ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne sojojin Bataliya suka yi gagarumin nasara wajen gudanar da ayyukan su wanda ya kai ga kwace manyan harsasai da haramtattun kayayyaki a kan iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin a ranar 12 ga watan Nuwamban 2023.
Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yaba wa sojoji akan taka-tsantsan da jajircewar su. Ya kuma bukace su da su ci gaba da dauwama a kan zaman lafiyar kasa domin ci gaban al’ummar Nijeriya baki daya.
Ladan Nasidi.