An sake zaben shugaban kasar Comoros Azali Assoumani a wa’adi na hudu a zaben da ‘yan adawa ke takaddama a kan shi a matsayin “magudi”.
Ya samu nasarar ne da kashi 63% na kuri’un da aka kada, in ji hukumar zaben Ceni.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, ‘yan takaran adawa a tsibirin tekun Indiya sun yi zargin cewa an yi amfani da kuri’u a zaben Mr Assoumani kuma an rufe rumfunan zabe da wuri.
Tawagar yakin neman zaben Mr Assoumani ta musanta ikirarin ‘yan adawa.
‘Yan takara shida ne suka fafata a zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 14 ga watan Janairu.
Mouigni Baraka Said Soilihi, daya daga cikin masu adawa da Mr Assoumani, an ruwaito yana cewa “Ba za mu iya magana kan sakamako ba saboda ba ayi zabe.”
Sama da mutane 330,000 ne aka yi wa rijista don kada kuri’a, daga cikin al’ummar da bankin duniya ya kiyasta ya kai 836,000.
Mista Assoumani tsohon hafsan soja ne wanda ya fara hawan mulki ta hanyar juyin mulki a shekarar 1999 kuma ya lashe zabensa na farko a shekara ta 2002.
Ya fice daga siyasa a shekarar 2006, kafin ya sake samun nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2016.
Ya samu damar neman wa’adi na hudu bayan kuri’ar raba gardama mai cike da cece-kuce ta kawar da iyakokin wa’adin shugaban kasa a shekara ta 2018, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a kasar.
Mulkin Mista Assoumani dai ya fuskanci cece-kuce, inda masu sukar sa ke zarginsa da daure abokan hamayyarsa gudun hijira.
Shi ne shugaban kungiyar Tarayyar Afirka a halin yanzu.
BBC/Ladan Nasidi.