Dalibai a yankin Kashmir da ke Pakistan, POK, sun yi zanga-zangar nuna adawa da tsadar ilimi.
Daliban da ke zanga-zangar adawa da karin kudin da ba a taba yin irinsa ba, suna kira ga hukumar da ta duba tsarin ilimi mai tsada.
Suna zargin cewa hukumar jami’ar na karya manufofin hukumar manyan makarantu ta HEC ta hanyar kara kudin karatu na zangon karatu.
“Ana karbar Lakhs na Rupee duk bayan wata 3 ko 4 da sunan kudin semester,” a cewar daliban da suka yi zanga-zangar.
Ana yin haka ne don kada dalibai matalauta su samu ilimi. Talakawa ba su da kudin rayuwa; ta yaya za su samar da ingantaccen ilimi ga ’ya’yansu?” Daliban masu zanga-zangar suka ce.
Daliban sun yi zargin cewa gwamnatin Pakistan ta ki sauraron halaltattun bukatunsu da ma’aikatan ilimi.
Sun kuma yi zargin cewa gwamnati na kallon ilimi a matsayin barazana ga mamaye yankunan da take yi ba bisa ka’ida ba, saboda tsoron cewa ilimi zai iya baiwa ‘yan yankin damar fahimtar da kuma tabbatar da hakkokinsu na shari’a.
A cewar daliban da suka gudanar da zanga-zangar Pakistan ba ta taba mayar da hankali kan koyo da wayewa a jihar ba, musamman a fannin ilimi a yankin Kashmir da Pakistan ta mamaye.
Daliban sun ce duk da tsananin bukatar samar da ingantattun kayan aiki, dalibai da ma’aikata a fannin ilimi ana nisantar da su daga ‘yancinsu na yau da kullun, a daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ke kara tabarbarewa, ma’aikatan koyarwa da gudanarwa na PoK na neman karin albashin da aka dade ba su yi ba.
Ma’aikatan ilimi sun yi kira ga kananan hukumomi da na tarayya sau da yawa, amma har yanzu bukatunsu ba su cika ba.
Ma’aikatan a bangaren ilimi sun bayyana karara cewa zanga-zangar ba za ta tsaya ba har sai an biya su karin albashin da suke da hakki a doka.
Ladan Nasidi.