Wata gobara da ta tashi a wani dakin kwanan dalibai da ke tsakiyar China ta kashe dalibai 13 tare da raunata wani mutum guda.
Rahoton ya ce wadanda suka mutu ‘yan aji uku ne, wadanda yawanci ‘yan shekara 9 ne. Mutum daya da aka ceto daga wurin yana jinya a asibiti
Gobarar ta tashi ne a daren Juma’a a makarantar Yingcai da ke kauyen Yanshanpu, kusa da birnin Nanyang a lardin Henan.
Rahotanni sun ce jami’an kashe gobara sun yi gaggawar kashe gobarar, kuma an tsare shugaban makarantar.
A halin da ake ciki, hukumomin yankin sun ce suna gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar.
Yingcai wata makarantar kwana mai zaman kanta tana ba da kulawa ga ɗalibai a matakin farko, kodayake tana da makarantar kindergarten, bisa ga shafin WeChat na makarantar. Da yawa daga cikin daliban kwana sun fito ne daga yankunan karkara.
Makarantar tana ba wa dalibai hutu kowane mako biyu amma wannan ba hutun karshen mako ba ne, kamar yadda manema labarai suka ambato mazauna yankin da dama.
REUTERS/Ladan Nasidi.