Harin Da Isra’ila Ta Kai Damascus Ya Kashe Jami’an Tsaron Farisa

Wani harin makami mai linzami da Isra’ila ta kai kan Damascus babban birnin kasar Sham ya kashe wani jami’in kare juyin juya halin Musulunci na Farisa tare da raunata wasu, kamar yadda wata majiyar tsaro a kawancen kasashen yankin da ke goyon bayan Sham ta sanar.
Kafofin yada labaran kasar Syria sun ce wani harin da Isra’ila ta kai ya kai wani gini da ke unguwar Mazzeh a birnin Damascus, ba tare da bayar da karin bayani ba.
Yayin da wasu kafafen yada labarai na cikin gida a Sham suka bayar da rahoton cewa an ji karar fashewar wasu abubuwa a fadin babban birnin kasar ta Sham.
Majiyar tsaron, wani bangare na kungiyoyin da ke kusa da gwamnatin Sham da kuma babbar kawarta Farisa, ta ce masu ba da shawara Farisawa masu goyon bayan gwamnatin Bashar al-Assad ne suka yi amfani da ginin bene mai hawa biyu, kuma gaba daya an lallasa shi da “makaman Isr’ila masu linzami.”
Babu wani karin haske daga Isra’ila.
Shugaban Asibitin Al-Mowasat da ke Damascus, Essam Al-Amin ya shaidawa manema labarai na kasar cewa asibitinsa ya karbi gawa daya da wasu mutane uku da suka jikkata ciki har da mace daya bayan harin.
Sai dai kuma mai magana da yawun kungiyar Jihad Islama ta Falasdinu ya shaidawa manema labarai cewa, babu wani dan kungiyarsu da ya samu rauni a harin, biyo bayan rahotannin da ke cewa wasu na cikin ginin da aka kai harin.
Isra’ila dai ta dade tana ci gaba da kai hare-haren bama-bamai kan wuraren da ke da alaka da Farisa a Sham. Amma ta koma kai munanan hare-hare bayan harin da mayakan kungiyar Hamas ta Falasdinu da ke samun goyon bayan Farisa suka kai wa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba.
A cikin watan Disamba, wani harin da Isra’ila ta kai ya kashe jami’an tsaro biyu, wani kuma a ranar 25 ga watan Disamba ya kashe wani babban mai ba da shawara ga masu tsaron da ke sa ido kan hadin gwiwar soji tsakanin Sham da Farisa.
REUTERS/Ladan Nasidi.