Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta dorawa Hukumar ba da Tallafin Karatu ta Jihar Nasarawa (NSSB) alhakin wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen hukumar ta fannin bincike da sanin makamar fasahar zamani domin samar da damammaki ga jama’a a jihar.
Mataimakin shugaban hukumar (EVC) Farfesa Umar Danbatta ne ya bada wannan aiki a wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a Reuben Muoka ya fitar a Abuja.
Daraktan tattalin arziki na dijital a hukumar Dr. Augustine Nwaulune Wanda ya karbi bakuncin tawagar hukumar karkashin jagorancin babbar sakatariyar hukumar Misis Saadatu Yahya a madadin hukumar ta EVC ya tunatar da cewa jihar Nasarawa na daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin na ayyukan Sadarwa da Fasahar Sadarwa (ICT) NCC.
Wasu daga cikin ayyukan sune; da Digital Awareness Programme (DAP) don makarantun sakandare, da Advanced Digital Appreciation Program Don jami’o’i (ADAPTI), da Wireless Cloud, da kuma shirin E-Health.
Ya ce: “Duk da cewa ba mu bayar da tallafin karatu ga dalibai, Hukumar NCC ta ci gaba da ba da tallafin bincike ga malamai da daliban jami’o’i, tare da bayar da karin damammaki da suka hada da daukar nauyin gasar da ta shafi dalibai, da kuma ba da kujerun farfesoshi a jami’o’in da ke fadin kasar”.
“A cikin shekaru bakwai da suka gabata, kudin tallafin da aka bayar ya haura Naira miliyan 500 ”
Ya Kara da cewa; “Don haka, zan yi kira ga NSSB da ta wayar da kan jama’a game da wadannan tsare-tsare na NCC a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, musamman tallafin bincike don baiwa masu ruwa da tsaki damar yin amfani da irin wannan damar da Hukumar ta ba wa masana masu sha’awar gudanar da bincike ta hanyar sadarwa.”
Nwaulune ya ce hukumar ta NCC ta himmatu wajen tabbatar da aiwatar da Manufofin Tattalin Arziki na Dijital na Kasa (NDEPS), 2020-2030, wanda daga cikin ginshikan ta guda takwas, daya ya dogara ne akan ilimin naurar Zamani, yayin da aka kafa Sashen Tattalin Arziki na Digital da kuma samar da kayan aiki na hukumar tare da albarkatun ɗan adam da ake buƙata don daidaita shirye-shiryenta a zahiri.
Yahya, wanda tawagarsa ta kai ziyara domin tattaunawa kan bangarorin hadin gwiwa domin zurfafa koyar da sana’o’in zamani a jihar Nasarawa, ya yabawa hukumar bisa rawar da ta taka wajen bunkasa wayar da kan jama’a da fasahar zamani a fadin kasar nan, ya kuma roki cewa a Bawa jihar Nasarawa damammaki don cin gajiyar sa hannun jarin NCC na zamantakewa da sauran ayyukan da suka shafi tattalin arziki na naurar amani, kasancewar ta Jiha mafi kusanci da Babban Birnin Tarayya, tushe na Hukumar.
Ya ce “Manufar ziyarar tamu ita ce neman hadin gwiwa da hukumar NCC ta kowace hanya, musamman a fannin bayar da tallafin karatu, da fasahar ICT da karantarwa ga mutanenmu.
“A yau, ICT na da dumbin muhimmancin wurin tattalin arzikin duniya kuma ba ma so mu yi la’akari da wannan sabon tsarin dijital, don haka, shawararmu na neman haɗin gwiwa tare da kungiyoyin ICT kamar ku don yin aiki musamman saboda Kuna makwabta da Jihar mu,” in ji Yahya.
Leave a Reply