Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce wani jirgin soji ya yi hatsari a Belgorod, kusa da kan iyakar Yukrai.
Ma’aikatar ta ce “A cikin jirgin akwai jami’an sojin Ukraine 65 da aka kama da ake jigilar su domin yin musaya, da ma’aikatan jirgin shida da mutane uku ‘yan rakiya.”
Gwamnan yankin ya ce babu wanda ya tsira, har yanzu kafafen yada labarai ba za su iya tantance wadanda ke cikin jirgin ba, ko kuma abin da ya jawo hatsarin jirgin.
Bidiyon da aka tabbatar ya nuna wani jirgin sama yana gangarowa kusa da kauyen Yablonovo, mai tazarar kilomita 70 zuwa arewa maso gabashin Belgorod.
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta zargi Yukrain da harbo jirgin amma ba ta bayar da wata shaida ba.
A halin da ake ciki, ana shirin musayar fursunoni tsakanin Rasha da Yukrain a yau, kamar yadda mai magana da yawun hukumar leken asirin sojin Yukrain ya shaida wa gidan rediyon Liberty.
An ambato Andriy Yusov yana cewa: “Zan iya bayyana cewa musayar da aka shirya yi a yau ba ta gudana ba tukuna.”
Ya kara da cewa ana duba bayanan da Rasha ta bayar na cewa fursunonin yaki na cikin jirgin da ya fado a Belgorod.
BBC/Ladan Nasidi.