Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa a ranar Laraba, 24 ga watan Janairu domin wata ziyarar sirri.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale, ya sanyawa hannu a ranar Laraba.
Shugaba Tinubu zai dawo Najeriya a makon farko na watan Fabrairun 2024.
Ku tuna cewa shugaban na Najeriya ya karbi bakuncin sakataren harkokin wajen Amurka, Anthony Blinken a ranar Talata a fadar shugaban kasa.
Shugaban na Najeriya a ganawar da yayi da Sakatare Blinken ya bukaci goyon bayan Amurka kan kasancewar Najeriya mamba a kungiyar G20 da kuma neman kujerar ta a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.
Ladan Nasidi.