A wata tattaunawa da Muryar Najeriya ta wayar tarho, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Chikun/Kajuru na tarayyar Najeriya, ya ce gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, ya amince da bayar da fili mai fadin hekta 25 domin kafa karamin filin wasa da zai dauki nauyin makarantar koyar da wasanni a mazabar Jiha.
Shugaban kwamitin wasanni na majalisar wakilan Najeriya Honorabul Ekene Aboubakar Adams na shirin cika daya daga cikin alkawuran yakin neman zabensa wanda shine kafa makarantar koyar da wasanni ta duniya a mazabarsa.
Hon. Adams ya godewa Gwamna Sani bisa goyon bayan wannan gagarumin aikin, wanda ya ce za a yi amfani da shi wajen jawo kananan yara da kuma renon su tauraro.
“Ina son godewa Gwamna Uba Sani kan wannan aiki, domin shi mutun mai son wasanni ne kuma yana da manufa daya na amfani da wasanni wajen karfafa matasa a jihar Kaduna,” Hon. Adams yace. “Muna so mu yi amfani da Wasannin Makaranta don fitar da matasa daga kan tituna.”
“Zuwar Shugaban Hukumar FIFA, da sauran fitattun jaruman wasanni da kuma tsaffin ‘yan wasan Super Eagles za su canza alkiblar matasanmu. Sakamakon dogon lokaci na wannan zai kai ga raguwar ayyukan fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma lalata.”
“Cibiyar Wasanni za ta hada gwiwa da manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai kamar Manchester United, Atletico Madrid da sauransu. Nan da ‘yan makonni masu zuwa ma’aikatar wasanni za ta koma wurin” Hon. Adams ya kara da cewa.
Dan majalisar ya ce shugaban FIFA Gianni Infantino, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Ibrahim Gusau, tsohon kocin Chelsea da Real Madrid, Jose Mourinho, fitattun ‘yan wasan Faransa da Brazil Zinadine Zidane da Ronaldo de Lima, fitaccen dan wasan golf na Amurka Tiger Woods da ‘yar wasan Tennis Serena Williams za su halarci gasar kafa harsashin ginin cibiyar wasanni.
Kara karantawa: FIFA da NFF sun kaddamar da karamin filin wasa a jihar Kebbi
Wasu fitattun masu kula da kwallon kafa irin su Mallakin kungiyar kwallon kafa ta Remo Stars, Hon. Kunle Soname, Shugaban FC Ebedei, Churchill Oliseh da sauran manyan masu ruwa da tsaki za su ba da shawarwari kan yadda makarantar za ta iya kokarinta.
Fitattun ‘yan wasan Afrika da Super Eagles, Didier Drogba, Samuel Eto, Elhadji Diouf, Austin Okocha, Garba Lawal, Daniel Amokachi, Peter Rufai, Victor Ikpeba da sauran dandazon jama’a ana sa ran za su halarci bikin.
hazikin mai kula da wasan kwallon kafa ya bayyana cewa ma’aikatar raya wasanni ta tarayya ta shigar da aikin a cikin kasafin kudin ta na shekarar 2024, wanda ke nuni da cewa an fara shirin.
Idan dai ba a manta ba, a lokacin yakin neman zaben shi na tunkarar zaben 2023, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Chikun/Kajuru na tarayya ya yi alkawarin samar da makarantar koyar da wasanni a yankin, inda ya jaddada kudirinsa na cika alkawuran zabe.
Ladan Nasidi.