Take a fresh look at your lifestyle.

Italiya Ta Dakatar Da Bayar Da Kudaden UNRWA

116

Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani ya bayyana cewa, kasar Italiya ta yanke shawarar dakatar da baiwa hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu UNRWA kudade.

 

Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan zargin cewa wasu ma’aikatan UNRWA na da hannu a hare-haren da kungiyar Hamas ta Falasdinu ta kai a Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, ko da yake Tajani bai yi magana kai tsaye kan wadannan zato ba.

 

“Gwamnatin Italiya ta dakatar da ba da tallafin UNRWA bayan mummunan harin da aka kaiwa Isra’ila a ranar 7 ga Oktoba,” Tajani ya buga a dandalin sada zumunta na X, ya kara da cewa wasu daga cikin abokan Italiya sun riga sun dauki wannan shawarar.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.