Ma’aikatar lafiya ta jihar Legas da karamin ofishin jakadancin jamhuriyar jama’ar kasar Sin sun gudanar da aikin tiyatar ido kyauta ga yara takwas domin magance matsalar idanuwa da suka makanta.
KU KARANTA KUMA: Cibiyar Ido ta Jihar Kaduna ta fara aikin tiyatar gyaran fuska
Babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Legas, Dakta Olusegun Ogboye, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa dauke da sa hannun Tunbosun Ogunbanwo, Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar a ranar Lahadi a Legas, inda ya ce taron na da nufin dawo da idanun mazauna yankin musamman kananan yara.
“Manufar wannan wayar da kan jama’a ita ce tabbatar da kyakkyawar makoma ga yaran da ke fama da ciwon ido.
“Gwamnati ta himmatu wajen inganta hanyoyin samun ingantattun ayyukan kula da ido da kuma hana makanta da za a iya kaucewa,” in ji Ogboye.
Ya ce ma’aikatar ta gudanar da ayyuka da dama a karkashin shirin rigakafin makanta na jihar don tallafawa harkokin kiwon lafiya na yau da kullun ga marasa galihu.
Ogboye ya yabawa karamin ofishin jakadancin kasar Sin da kungiyar jama’a da kamfanoni na kasar Sin bisa hadin gwiwar da suke yi.
Har ila yau, Mr. Lei Yu, wakilin karamin jakadan kasar Sin, ya ce mambobin al’ummar Sinawa dake Najeriya suna kallon Najeriya a matsayin gidansu, kuma za su ba da taimako da zai inganta rayuwar mabukata.
“Wannan shi ne mafari kuma za mu ci gaba da kara kaimi, kuma baya ga aikin tiyatar ido kuma muna yin abubuwa da yawa a fannin ilimi,” in ji shi.
Yu ya yabawa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da ta bayar wajen samun nasarar shirin aikin tiyatar ido kyauta.
Hakazalika, Mista Temitope Tomiluyi, mahaifin biyu daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin, ya nuna jin dadinsa da wannan shiri na abin yabawa, inda ya ce ‘ya’yansa tagwaye sun amfana da aikin tiyatar ido kyauta.
“Mun ziyarci manyan asibitocin Ijede da Epe, an gudanar da gwaje-gwaje da yawa a kansu, kuma an gano cewa cutar ta kusa rufe idanunsu.
“Kudin yin aikin ido daya yana da yawa sosai, ba maganar tiyatar idanu hudu ba.
“Mun zo nan a ranar Litinin kuma an gaya mana cewa za a gudanar da aikin a ranar Juma’a kuma an biya dukkan kudaden da aka kashe,” inji shi.
Ladan Nasidi.