Take a fresh look at your lifestyle.

Za’a Gudanar Da Bikin Al’adun Jihar Kebbi Na Yauri A Ranakun 8 zuwa 10 Ga Fabrairu, 2024

Binta Aliyu,Kebbi.

501

Shahararren bikin al’adun Yauri na wasan kwale-kwale na jihar Kebbi karo na uku ne zai gudana a tsohon birnin Yelwa-Yauri a ranakun 8 zuwa 10 ga watan Fabrairun bana.

 

Shugaban bikin na kasa kuma sakataren gwamnatin jiha Alhaji Yakubu Bala Tafida ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi.

 

Ya ce taron zai gabatar da kaddamar da littafin tarihin Yauri daga shekarar 1411 zuwa yau da kasuwar baje kolin kayayyakin al’adun gargajiya.

 

Alhaji Yakubu Bala Tafida ya ce daukar bikin nuna al’aladun was an ruwa da gwamnatin jihar Kebbi ta yi a matsayin babban taron al’adu ya samu asali ne ta hannun Sarkin Yauri na 42 na yanzu, Dakta Muhammad Zayyanu Abdullahi ya kuma ce Wasan ruwa kalma ce a yaren ‘yan kabilar Gungawa da ke nuna bikin yakin ruwa da aka fara a shekara ta 200. Shekarun da suka gabata a wani baje kolin karfin sojan ruwa na mayaka sun kai hari a kan kogin Nijar mai hatsarin gaske.

 

Sakataren Gwamnan Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafida ya kuma ce zuwan Turawa ne ya sa gwamnatin mulkin mallaka ta hana farautar domin kare irin wannan dabi’a har zuwa ziyarar marigayi Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sokoto zuwa Yelwan -Yauri inda aka shirya bikin kamun kifi tare da nuna albarkatun gona domin karrama shi.

 

 

Binta  Aliyu.

Comments are closed.