Uwar Gidan Gwamnan jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda ta kaddamar da rabon magani kyauta ga masu fama da lalurar sikila a jihar
Uwar gidan gwamnan ta kuma kaddamar da rabon maganin cutar zazzabin cizon sauro hadi da gidan sauro mai dauke da maganin ga wadanda ke fama da lalurar
Bikin rabon kayan wanda ya gudana a babbar asibiti wato general hospital dake birnin Katsina ya samu halartan kwamishinan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya dake jihar
A jawabinta a wajen taron uwar gidan gwamnan, Zulaihat Radda ta bayyana tausayinta ga masu fama da lalurar tana mai bada tabbacin ta na cigaba da tallafawa masu lalurar domin rage masu radadin da cutar ke haifar masu tare da nuna masu cewa gwamnati da al’umma na tare da su
Zulaihat Radda wadda ta bayyana damuwarta akan yadda wani bincike ya nuna cewa Najeriya tana akan gaba wajen dauke da masu fama da lalurar sikilar ta kuma jaddada bukatar da ke da akwai ga masu ruwa da tsaki wajen dakile yawan masu kamuwa da cutar
Tace za’a iya kawo karshen cutar ne idan mahukunta da al’umma suka bada hadin kai wajen bin matakan rigakafin kamuwa da ita musamman ta hanyar yin gwaji kafin yin aure domin ma’aurata su kaucema auren junan da ka iya haifar yara masu dauke da cutar a cikin jininsu
Shima a nasa jawabin a wajen taron, kwamishinan ma’aikatar lafiya na jihar Katsina, Dr. Bashir Gambo Saulawa shima bayyana damuwar sa yayi akan irin radadin da masu lalurar ke fama dashi a duk lokacin da lalurar ta tasar masu, musamman rasa wasu sassan jikinsu sakamakon lalurar
Daga nan sai ya bukaci al’ummar jihar dasu tallafawa shirin gwamnatin jihar na kokarin Inganta lafiyar su
Kwamishinann yayi kira garesu da su rika yin gwaji irin halittar jininsu a lokacin da ya dace domin kare yara masu tasowa daga kamuwa da cutar ta sikila a jihar da Najeriya baki daya.
Kamilu Lawal.