Take a fresh look at your lifestyle.

Hari Da Wuka Ya Raunata Mutane Uku A Paris

73

 ‘Yan sanda sun ce wani harin wuka da aka kai a tashar jirgin kasa ta Gare de Lyon da ke birnin Paris ya yi sanadin jikkatar mutane uku.

 

Sun ce sun kama wanda ake zargi da kai harin.

 

Biyu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun samu raunuka kadan yayin da na ukun ya samu munanan raunuka amma ba ya cikin wani yanayi na barazana ga rayuwa, in ji ‘yan sandan.

 

A halin da ake ciki, ba a fayyace dalilin wanda ake zargi da kai harin ba.

 

Faransa ta sha fama da hare-haren masu kishin Islama a cikin shekaru goma da suka gabata, amma kuma a wasu lokuta ana kai hare-hare daga masu fama da tabin hankali.

 

Rahoton ya ce wanda ya kai harin a Gare de Lyon a safiyar ranar Asabar dan kasar Mali ne kuma yana dauke da lasisin tuki dan kasar Italiya, kamar yadda wata majiyar ‘yan sanda ba ta bayyana sunanta ba. Ba a kai ga tabbatar da wannan rahoton ba.

 

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.