Take a fresh look at your lifestyle.

KUNGIYAR KWALLON KAFA TA EAGLED ZATA CI GABA DA NUNA KWAZO A WASA DA SUDAN

0 403

Kocin kungiyar kwallon kwallon kafa ta Super Eagles sun lashi takobin ci gaba da nuna kwazon samun nasara a gasar cin kofin Afirka tsakanin ta da kasar Sudan,wasan dake gudana a birnin Garoua na kamaru a ranar asabat.
A halin yanzu dai Najeriya na Rukuni na D tare da maki Uku, Sudan da Guinea Bissau nada maki guda kowannen su kana Masar na nema.
Idan har Najeriya ta samu nasara a was an gaba na rukunin 16 to zata ji dadin wasa na gaba.
Kocin kungiyar Eagles Augustine Eguavoen ya sanarwa manema labarai cewa sun shirya gudanar da kowane wasa tamkar buga wasan cin kofi na karshe.
Mataimakin shi, Salisu Yusuf yace yana ganin was an da zaa gudanar tsakanin tad a Sudan zai kasance mai zafi,amma na wasa da kasar Masar ba zai zama mawuyaci ba gakamar was an farko.
Kaptin Ahmed Musa ya nunawa kocin cewa sun lashi takon ba zasuyi kasa a guiwa wajen dauko wannan kofin.
Hakazalika yan wasan sun samu karfin guiwar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wanda ya bukace su suci gaba da nuna kwazon su wajen gasar saboda miliyoyin yan Najeriya na taya su adduar samun nasarar lashe kofin Afirka.
Shi ma Ministan wasanni , Sunday Dare kira yayi gare su das u rinka kula da kwsalon da suke bugawa kada su bari masu kallo su janye hankalin su.

Ladan Nasidi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *