Take a fresh look at your lifestyle.

Ukraine: Zelenskiy Ya Ziyarci Sojojin Da Ke Fagen Yaki

86

Shugaban kasar Volodymyr Zelenskiy ya ziyarci sojojin Ukraine da ke yankin kudu maso gabas tare da raba lambobin yabo.

 

Kakakin nasa ya ce ya kusa yin musayar wuta a fagen daga a lokacin ziyarar tasa.

 

Zelenskiy ya yi tafiya zuwa yankin Zaporizhzhia a cikin rade-radin cewa nan ba da jimawa ba za a iya korar fitaccen hafsan sojan sa.

 

Shugaban, wanda ya rika zagayawa yankunan da ke kusa da gaba, ya gana da sojoji a kauyen Robotyne, kamar yadda ofishinsa ya ce, kusan a fagen daga.

 

Kakakin shugaban kasar Serhiy Nikiforov ya shaidawa manema labarai cewa “Wannan Robotyne ne kuma ana gwabza kazamin fada.” Saboda haka yana kusa da fashe-fashe, amma ba zan yi wasa da yanayin ba.”

 

Sojojin Ukraine da aka ambato a shafukan sada zumunta sun ce yankin da Zelenskiy ya ziyarta na da kasada saboda tsananin ayyukan jirage marasa matuka.

 

Zelenskiy a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce ya zo yankin ne domin tallafawa da kuma karrama sojojin Ukraine.

 

“Suna fuskantar wani aiki mai wahala da mahimmanci don fatattakar abokan gaba da kare Ukraine,” in ji shi.

 

A karshen watan Agustan shekarar da ta gabata ne aka kwato matsugunan Robotyne na Kudu maso Gabashin kasar a wani farmaki da aka kaddamar kan sojojin Rasha. A dunkule gaba daya, farmakin na kai hare-hare ya samu takaitaccen nasara wajen kwato yankunan da sojojin makiya suka tona sosai.

 

Ziyarar a fagen daga na gudana ne a daidai lokacin da ake cikin rashin tabbas kan makomar hafsan sojin kasar Valeriy Zaluzhnyi.

 

 

 

REUTERS/Ladan Nasidi.

Comments are closed.