Take a fresh look at your lifestyle.

Gaza: Hamas Ta Mayar Da Martani Ga Shawarwarin Sulhu

124

Hamas ta ce ta mayar da martani ga wani tsari na tsagaita bude wuta a Gaza.

 

Ba a fitar da cikakkun bayanai kan yarjejeniyar da Isra’ila, Amurka, Qatar da Masar suka kulla ba.

 

Tun da farko an ba da rahoton hada da tsagaita wuta na tsawon makonni shida, lokacin da za a yi musayar wasu karin mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su da fursunonin Falasdinu.

 

Isra’ila da Amurka duk sun ce suna nazarin martanin Hamas.

 

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, wanda a halin yanzu yake Gabas ta Tsakiya, ya ce zai tattauna martanin Hamas da jami’ai a Isra’ila.

 

Yayin da Mista Blinken bai bayar da wata alama ta yadda Amurka ke kallon martanin ba, Shugaba Joe Biden ya bayyana shi a matsayin “dan kadan a kan gaba” yana mai nuni da cewa shugabancin Isra’ila ba zai amince da abin da kungiyar ke tambaya ba cikin sauki.

 

Wani babban jami’in Hamas ya ce kungiyar ta gabatar da “hanyar hangen nesa” domin mayar da martani ga tsarin amma ta nemi wasu gyare-gyaren da suka shafi sake gina Gaza, mayar da mazaunanta gidajensu da kuma tanadi ga wadanda aka raba.

 

Jami’in ya ce Hamas ta kuma bukaci a yi sauye-sauyen da suka shafi kula da wadanda suka jikkata, da suka hada da komawa gida da mika su zuwa asibitocin kasashen waje.

 

Firayim Ministan Qatar Sheikh Mohammed Bin Abdulrahman al Thani ya bayyana martanin Hamas a matsayin “mai kyau” gabaɗaya.

 

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Comments are closed.