Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Dakta Abbas Tajudeen, zai gudanar da taron manema labarai na duniya kan wasu batutuwan da suka shafi kasa baki daya ranar Alhamis a Majalisar dokokin kasar.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban majalisar shawara kan harkokin yada labarai Musa Abdullahi Krishi ya fitar ranar Laraba a Abuja.
Sanarwar ta ce taron manema labaran zai maida hankali a akan sha’anin tsaro, tattalin arziki, da dai sauransu, ya kuma kara da cewa ana sa ran ‘yan jarida daga ciki da wajen majalisar za su hallara domin daukar rahoto kan taron.
Sannan ya bayyana cewa za a watsa shi kai tsaye a shafin Facebook na majalisar wato https://www.facebook.com/HouseNGR, da shafukan sada zumunta na shugaban majalisar a Facebook da Instagram wato https://www.facebook.com/HonAbbasTajudeenPhD da https://www.facebook.com/HonAbbasTajudeenPhD ://www.instagram.com/speakerabbas?igsh=aXhscXpkMW5zejl5, da kuma NASS TV a tashar ta YouTube.
Abdulkarim Rabiu