Shugaba Vladimir Putin ya ce ya yi imanin za a iya cimma yarjejeniya da zata sako Evan Gershkovich, dan jaridar Amurka da aka tsare a bara a Rasha.
Da yake magana da mai masaukin baki na Amurka Tucker Carlson, Putin ya ce ana ci gaba da tattaunawa da Amurka game da dan jaridar da ake tsare da shi kan zargin leken asiri.
A cikin hirar, Putin ya yi magana kan Yukrain, shugabannin Amurka da CIA.
Wannan dai shi ne karon farko da shugaban na Rasha ya zauna da wani dan jarida na yammacin duniya tun bayan da Rasha ta mamaye Yukrain a shekarar 2022.
Putin ya ce ya yi imanin za a iya kulla yarjejeniya da zata saki Gershkovich, mai shekaru 32, “idan abokan aikin mu suka dauki matakan daidaitawa”.
“Ayyukan na musamman suna hulɗa da juna. Suna Magana kuma na yi imani za a iya cimma yarjejeniya.”
An kama Gershkovich, dan jarida na jaridar Wall Street Journal a birnin Yekaterinburg, kimanin kilomita 1,600 (mil 1,000) gabashin Masko, a ranar 29 ga Maris din shekrar da ta gabata.
A watan Janairu, Rasha ta sake tsawaita tsare shi kafin a yi masa shari’a har zuwa karshen watan Maris. Idan aka same shi da laifi zai fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekaru 20.
BBC/Ladan Nasidi.