Take a fresh look at your lifestyle.

GBV: Jihar Adamawa, UNICEF Ta Horar Da Matasa 2,260

146

Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Adamawa, tare da hadin gwiwar Asusun Kula da kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), sun horar da matasa 2,260 kan cin zarafin mata (GBV).

 

KU KARANTA KUMA: GBV: Cibiyar Katsina na kula da masu cuta guda 10 a cikin wata guda

 

Jami’ar tsare-tsare ta Jihar, Matasa da Lafiyar Jima’i, Hajiya Fadimatu Hamman-Joda, ta bayyana haka a wata tattaunawa da ta yi da manema labarai a Yola, inda ta ce an zabo wadanda aka horas da su cikin tsanaki a sassan zabe 226 na jihar, inda ta kara da cewa an yi wa mutum 10 rajista daga kowace shiyya.

 

Ta bayyana cewa an wayar da kan mahalarta taron kan illolin karkatattun halaye kamar fyade, shaye-shayen miyagun kwayoyi, shaye-shaye da rigingimun da ba dole ba, da dai sauransu.

 

“Za’ a tura wadanda aka ba horon zuwa kananan hukumomi 21 na jihar domin yin amfani da ilimin da aka samu wajen zaburar da matasa 2,203.

 

“Shirin ya yi niyyar horar  da matasa 4,000 nan da shekara ta 2024.”

 

Sai dai ta ce rashin isassun kayan aiki yana shafar aiwatar da shirin.

 

Ta yaba wa gwamnatin jihar da hukumar UNICEF bisa goyon bayan shirin.

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.