Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da kawar da ‘yan bindiga da suka hada da mai garkuwa da mutane mai suna Musa Wada (Sabo) Magaji, a wani samame da aka gudanar a kusa da Mpape a Abuja, babban birnin kasar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa, ya kuma bayyana cewa rundunar ta lalata sansanonin masu garkuwa da mutane.
“Yan bindigar dauke da makamai sun yi artabu da jami’an ‘yan sanda a wani artabu na kusan mintuna 30, wanda ya yi sanadin jikkatar da dama daga cikin ‘yan bindigar, yayin da daya daga cikin ‘yan sandan ya samu raunuka.
“Wannan gagarumar nasara ta biyo bayan kashe Abubakar Wada, wani abokin Musa Wada, a ranar 8 ga Fabrairu, 2024, wanda ya kai ga maboyar su”.
“Musa Wada, wanda aka fi sani da Sabo, shi ne ya jagoranci sace-sacen mutane da dama don ayyukan kudin fansa da suka addabi yankunan da suka hada da Mpape da Bwari a babban birnin tarayya Abuja; Kagarko a Kaduna; Masaka, da kuma kauyen Nukun dake jihar Nasarawa. Modus operandi nasa ya hada da gano masu hannu da shuni da kuma hada gungun kungiyoyi masu dauke da makamai domin yin garkuwa da su domin neman kudin fansa.”
A cewarsa, farmakin da suka kai maboyar su da ke wajen tsaunin Mpape, an kai su ne ta hanyar wani harin ba-zata, wanda ya yi sanadin kawar da masu laifin.
“Abubuwan da aka kwato daga maboyar sun hada da wayoyin hannu, katunan SIM da yawa, laya, da kuma magunguna masu tsauri, wadanda muhimman shaidu ne da ke taimakawa a gudanar da bincike. Ana ci gaba da kokarin kwato karin makamai da alburusai da sauran kayan aikin da suke amfani da su wajen munanan ayyukansu.”
Adejobi, ya jaddada aniyar rundunar ‘yan sanda na yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan kasa baki daya
“Kuma zata cigaba da yin amfani da matakan da suka dace don wargaza hanyoyin sadarwa da kuma gurfanar da masu aikata munanan laifuka a gaban shari’a, ba tare da wata matsala ba.” Ya kara da cewa.