Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiyar ‘Yan Kasuwa Ta Abuja Ta Yi Zaman Makokin Herbert Wigwe

51

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Abuja (ACCI), Dakta Emeka Obegolu ya bayyana matukar bakin ciki da kaduwa sakamakon rasuwar babban jami’in kamfanin Access Holdings, Mista Herbert Wigwe.

 

Wigwe, tare da matar shi, dan shi, da abokan aikin shi, sun yi hatsari a cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu a ranar Juma’a.

 

Mista Obegolu, ya bayyana cewa labarin rasuwar Wigwe da na danginsa da abokan aikinsa ba babban rashi ne ga iyalinsa ba, har ma da bangaren bankin Najeriya da kuma ‘yan kasuwa baki daya.

 

“Wigwe, a matsayinsa na jagoran daya daga cikin manyan bankunan Najeriya, ya bar wani tarihi da ba za a taba mantawa da shi ba a harkar bankunan Najeriya da tattalin arzikin kasar, inda ya samu gagarumin sakamako,” in ji shi.

 

Mista Obegolu ya sake nanata cewa iyalan Access Bank, da bangaren bankunan Najeriya, da kuma ‘yan kasuwa sun yi babban rashi sakamakon rasuwar Wigwe, wanda ya yi suna da basira da kyawawan halaye.

 

Ya kuma ce; “Wannan rashi ya shafi duk wanda ya sami damar sanin Wigwe da kuma sanin irin gudunmawar da ya bayar ta hanyoyi daban-daban.”

 

Mista Obegolu ya kara da cewa, “A madadin majalisar zartarwa da mambobin kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Abuja (ACCI), ina yin addu’a ga wadanda suka rasu da kuma mika ta’aziyya ga iyalan su.”

 

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.