Take a fresh look at your lifestyle.

NFF Ta Nemi Karin Tallafin Kamfani Ga Kwallon Kafa Na Najeriya

214

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta yi kira ga kungiyoyi da su kara tallafawa hukumar don taimakawa wajen bunkasa kwallon kafa a kasar.

 

Shugaban hukumar ta NFF, Ibrahim Gusau ne ya yi wannan kiran a lokacin da MTN Nigeria ta karbi bakuncin Super Eagles, wadanda suka zo na biyu a gasar cin kofin Nahiyar Afirka da aka kammala na 2023, a wani taron karin kumallo ranar Talata a Abuja.

 

KU KARANTA KUMA: Ministan Wasanni Ya Kokarin Ci Gaban Polo A Najeriya

 

Eagles ta kare a matsayi na biyu da kasar mai masaukin baki wato Ivory Coast bayan ta sha kashi a hannun kasar da ci 2-1.

 

Shugaban Hukumar NFF Gusau ya ce tafiyar da kwallon kafa na da wahala ba tare da kudi ba.

 

Gusau, yayin da ya yabawa kamfanin sadarwa na MTN, ya kara da cewa, domin hukumar ta samu ci gaba a harkar kwallon kafa, ya kamata kungiyoyin kamfanoni su rika bayar da kudaden bunkasa kwallon kafa ta hanyar NFF.

 

“Dukkanmu a nan yau (Talata) da mun yi sha’awar a yi bikin a nan da kofin amma abin takaici Allah ya san dalili. Amma mun gode wa Allah, akalla kamar yadda muka ji daga bakin kyaftin din, wannan shi ne farkon wayewar gari dangane da harkar kwallon kafa ta Najeriya.

 

Babban Jami’in Kamfanin na MTN na Najeriya, Karl Toriola, ya yaba da jajircewar ‘yan wasan na samun nasara.

 

Babban mai horar da ‘yan wasan Super Eagles, Jose Peseiro, ya godewa duk wanda ya goyi bayan kungiyar a duk shirye-shiryen da suka yi da gasar yadda ya kamata.

 

 

Ladan Nasidi.

Comments are closed.